Ba Domin Zuwan Tinubu Ba Da Najeriya Ta Wargaje – Ministan Ayyuka

Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa da Najeriya ta wargaje, idan ba don Allah ya kawo shugaba Bola Tinubu karagar mulki a wannan lokaci mai muhimmanci ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya bukaci matasa da su soke zanga-zangar da suke shirin yi da kuma tallafawa Gwamanti wajen bunƙasa ababen more rayuwa.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin Gwamnatin Tarayya mai taken “Operation Free Roads” a Abuja a karshen mako, Umahi ya bayyana kwarin gwiwar cewa shugaban kasar zai kawo sauyi a kasar idan aka kara masa lokaci. Ya bayyana cewa shirin na da nufin tabbatar da cewa dukkan hanyoyin da ake ginawa suna da motsi da kuma kammala su cikin gaggawa.

“Bari na yi amfani da wannan dama domin in yi kira ga matasan mu da su kara wa shugaban kasa Bola Tinubu lokaci, da ta kasance kasa ta gaza da Allah bai kawo shugaban kasa ba a irin wannan mawuyacin lokaci, mutane da yawa ba su fahimci kalubalen da muka fuskanta a baya ba. inji shi.

Umahi ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu kishin kasa tare da marawa gwamnati baya a kokarin da take yi na sake dawo da kasar nan kan turba madaidaiciya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply