Wata shaidar gani da ido ta bada labarin abinda ya faru a kasuwar Shasha da ke Ibadan a jihar Oyo da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 20 da asarar dukiyoyin miliyoyin naira.
A bidiyon da ya bazu a ranar Litinin, wata shaidar gani da ido da ta ce sunanta Nana Aisha ta yi gyara game da ikirarin da aka yi da farko na cewa wani bahaushe ne ya kashe bayarabe inda ta ce wani dan Nijar ne, mai sana’ar tura baro.
Ta ce rikicin da ya faru tsakanin Hausawa da Yarbawa mazauna garin ya faru ne bayan wani dan Nijar ya zubar da tumatur a gaban shagon wata bayarabiya kuma ta dage sai ya wanke mata shagonta.
A lokacin da mutumin ke bata hakuri kafin ya samo ruwa, wani bayarabe ya tsoma baki a maganan ya kuma shararawa dan Nijar din mari.
Dan Nijar din ya rama marin inda bayaraben ya zame ya fadi a kasa ya kasa tashi. Daga nan ‘yan uwansa suka kai shi asibiti inda likitoci suka tabbatar da ya mutu.
“Daga nan ‘yan daban Shasha suka fusata suka fara kashe Hausawa. Suna tsammanin da gaske hausawa suka tada rikicin, ba su san cewa Dan Nijar ne ya mari wani har ya mutu ba.
Don haka ina shawartar ku da ku rika bincike kafin ku wallafa abinda ba dai-dai bane.
Abu daya da za a wallafa zai iya sanadin rikicin kabilanci. Rubutu daya ya janyo an kashe mutane da yawa,” a cewarta.
Ta kara da cewa rubutun da wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa na ikirarin cewa bahaushe ne ya kashe bayerabe ya tada rikicin kabilancin da ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi har ya kai ga gwamnati ta rufe kasuwar.