Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya ce an zabi gwamnatinsa ne domin ta ha?aka tare da raya jihar ba wai don ya biya albashi ba kawai.
Wannan na zuwa ne bayan korar ma’aikata kimanin 4,000 daga aiki a fadin kananan hukumomi 23 a fadin jihar.
Gwamnan ya kara da cewa “an zabe ni ne domin tabbatar da ingantattun damarmaki, na gina asibitoci da makarantu, na ha?aka abubuwan more rayuwa na kuma kare jihar, da samar da yanayin da zai iya jan hankalin masu kamfanoni su zuba jari don samar da ayyukan yi ga mutane”.
El-Rufa’i ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye ya ce yanayin samun kudin jihar ya ragu ta inda ta fi samun kudin shiga.
“A watan Nuwamba 2020, naira miliyan 162.9 ta yi wa Gwamnatin JIhar Kaduna ragowa bayan kammala biyan albashi, ta karbi N4.83bn daga FAAC ta kuma biya ma’aikata N4.66bn, a cewarsa.