A ranar Juma’a Ministan Sadarwa da raya tattalin Arziki na Digital Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ziyarci shahararran malamin dariqar Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi a gidan sa dake kofar Gombe a jihar Bauchi.
Yayin ziyarar Shehin Malamin ya yabawa Minista Pantami kan yadda yake gudanar da ayyukan shi kuma Malami mahaddacin Kuar’ani na farko da ya zamo minista a Nijeriya.
“Wannan abun alfahari ne a gare mu kuma muna yi masa fatan alheri”, inji shehin malamin.
“Hakika kai ɗa ne a wajena duk da yake kai ɗan Izala ne masu zagi da sukar Waliyyai”.