Ba A Taɓa Yin Adalin Shugaba A Najeriya Kamar Buhari Ba – Jiƙamshi

Shugaban hukumar Kula Da Zuba Hannun Jari ta Jihar Katsina Kuma Shugaban kwamitin wayar da Jama’a Kan Al’umma Jihar Katsina bisa ga shirye-shiryen tallafin da Gwamnatin Tarayya, Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana cewa tunda aka dawo mulkin damakaradiyyaamakaradiyya a kasar nan ba’a taba samun gwamnatin da ta bullo da shirye- shiryen tallafi da ta zizarawa yan Nijeriya kudade daban daban kamar ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ba.

Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana haka ne a dakin taro na hukumar EEC, da ke kan hanyar Kano a cikin garin Katsina, a lokacin da yake kaddamar da bada horan kwana daya ga jami’an kula da harkokin kasuwanci na kananan hukumomi talatin da hudu na jihar Katsina.

Jikamshi ya kara da cewa duba da dimbin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta bullo da su, da ke da manufar bunkasa kananan da matsakaitan sana’o’in a kasar nan. Alummar jihar nan sun rasa damarmaki da dama, na masu kananan sanaaoi da matsakaitan sana’o’in, saboda rashin zamanantar da sana’o’in su. Kimanin Kanana da matsakaitan sana’o’in dubu shidda da doriya ne za’a yi wa rijista.

Shugaban hukumar ya bayyana damuwarsa yadda al’umma kasar nan ba su nuna jin dadinsu bisa ga kin nuna godiyarsu ga kokarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na shirye shiryenta na tallafawa mutane bisa ga bunkasa kasuwancinsu. Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi kokari matuka wajen inganta rayuwar al’umma Nijeriya kuma dukkanin shirye-shiryen yana tafiya kai tsaye ba tare da nuna banbancin siyasa ba, ko bangaren ci ba, kai tsaye ta hanyar intanet ake cike mafi yawancin tsarin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply