An bayyana Uwargidan Shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari a matsayin wata Mace ta daban wadda a tarihin Najeriya ba a ta?a yin wata Uwargidan Shugaban Kasa kamar ta ba.
Mai girma Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da littafin Uwargidan Shugaban kasar wadda ya gudana a birnin tarayya Abuja, inda ya i Hajiya Aisha Buhari a matsayin matar da ta canza salon ofishin uwargidar shugaban kasa a tarihin Najeriya.
Farfesa Yemi Osinbajo ya na cewa Aisha Muhammadu Buhari mata ce wanda ta sha dabam da duk sauran takwarorinta da aka yi a baya, ta fuskar jajircewa wayewa da sanin ya kamata da haskaka rayuwa.
A cewar Osinbajo, dabi’ar Hajiya Aisha Buhari ne ya jawo mata farin-jini wajen al’ummar Najeriya. Osinbajo ya ce daga cikin inda Aisha Buhari ta banbamta da sauran matan shugabannin da aka yi a baya shi ne ta bude shafukan sada zumunta a kafafen zamani.
“Da wahala a ce an yi wata uwargidar shugaban Najeriya a baya wanda a cikin kankanin lokaci ta shiga zuciyar mutane sosai kamar Aisha Buhari.” “Ita ce uwargidar shugaban Najeriya ta farko da aka gani a shafin Twitter, Instagram da sauran dandalin sada zumunta na zamani, kuma aka san da zamanta.”
“Kuma watakila ita ce ta farko da ta ke samun ra’ayoyin ‘Yan Najeriya kai-tsaye.” “Da ra’ayoyinta na kai-tsaye da fadan gaskiya da wasu ke ganin sun sha banbam wasu lokutan, ta jawo abin magana wajen ‘Yan Najeriya da har yau ba a daina ba.”
Mataimakin shugaban kasar ya ce Uwargidar mai gidansa ta fita dabam a dalilin taimakon jama’a da ta ke yi, ya ce za a dade ba a manta da ita a tarihin kasar nan ba.