Ɗaya daga cikin shakikai, abokin Makarantar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuma Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na kasa na riko, Mai wakiltar Arewa Maso Yamma, Sanata Abba Ali ya bayyana cewa yadda ya san halin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na gaskiya da rikon amana, duk wanda ya kama da zanba cikin aminci ko satar dukiyar al’umma ko da dansa ne na cikinsa Ina da yakinin da sai ya hukunta shi muddin aka tabbatar yana da laifi, sai ya hukunta shi.
Sanata Abba, ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a gidansa dake Unguwar Yar’adua, cikin garin Katsina, dangane da halin da jam’iyyar APC take, a matakin kasa karkashin kwamitin riko, na Gwamna jihar Yobe Mai Mala Buni, wanda kuma a kwamitin shi ne Mai Wakiltar Arewa maso yamma.
Mataimakin Shugaban jam’iyyar na kasa ya cigaba da cewa kamar yadda kowa ya sani cin hanci da rashawa a kasar nan, ba lokacin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari aka fara shi ba, ya zo ya iske ya katutu a kasar nan, ba ki daya. Daman idan ka ce za ka yi yaki da shi akwai abokan hamayya da ke bin hanyar Kuma ba su so a gyara. Duk mutum ajizi ne, abinda na sani dangane da Muhammadu Buhari ko dan cikin shi ya kama da laifi sai ya hukunta shi.
Abba Ali ya kara da cewa, Shugaban Kasa Muhammadu ya shirya abubuwan alheran da gwamnatocin baya ba a yi su, duk da faduwar darajar mai, ya kawo asusun hada ka, Wanda ya dode hanyoyin sata da damar gaske, ga matasa an dauka na Npower ga tallafi iri-iri ga matsalar tsaron nan ana samun cigaba zaa matasa dubu dubu a kananan hukumomi dari bakwai da saba’in da hudu. Daman gyara dole ka gyarawa wani Kuma ka batawa wani. Yanzu dai mu ke rike da gwamnatin, sai mun yi sakaci za ta fita daga hannun mu kuma shi yasa muke son gyara kura kuranmu a jam’iyyan ce ya zo dai dai da raayin Jama’a,insha Allah za mu yi nasara a 2023.