Ba A Sa Niyyar Magance Matsalar Tsaro A Arewa Ba – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar IlI, ya bayyana yadda lamarin tsaro yake kara tabarbare a arewacin Najeriya, Sarkin Musulmi ya bayyana cewa yanzu ‘yan bindiga na cin karansu ba babbaka ba tare da an kawo karshen matsalar ba duk da asarar data ke kawo wa.

Mai alfarma Sarkin Musulmi wanda shine shugaban majalisar koli ta lamuran addini a Najeriya ya bayyana cewa yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna awon gaba da mutane a Arewa. Alhaji Sa’ad ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, yayin taron majalisar hadin kan addinai NIREC da akayi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito. Sultan yace: “Ba wai babu hanyar da za’a magance matsalolin ba ne. Kawai abinda muka rasa shine rashin niyya.”

Matsalolin tsaro sun dade suna addabar yankin arewacin kasar nan inda mafi yawancin masu sharhi ke gannin wallen gwamnati da masu ruwa da tsaki musamman a shugabancin yankin arewacin kasar nan.

Kuna ganin idan aka karfafa niyya kamar yadda mai alfarma sarkin musulmi ya bayyana za a iya kawo Karshen matsalar tsaro a arewa?

Labarai Makamanta

Leave a Reply