Ba A Cikin Fadar Shugaban Kasa Gobara Ta Tashi Ba – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ?ar?ashin jagorancin mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi ?arin haske da cikakken bayani game da rahotannin da ake ya?awa cewa gobara ta tashi a fadar shugaban ?asa ta Aso Villa Abuja, inda tayi mummunan ta’adi.

Fadar Shugaban kasan ta ?aryata wannan labarin inda ta bayyana shi a matsayin labarin ?anzon kurege da babu gaskiya a ciki, sai dai ana ya?a shi ne domin wata ?oyayyar manufa.

Mai magana da yawun Shugaban Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu shi ne ya bayyana hakan, a yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channel ya yi dashi dangane da yama?i?in da ake yi na tashin gobarar.

Garba Shehu ya ?ara da cewa duk da an samu tashin wata wuta kusa da fadar Shugaban kasan amma ko ka?an wutar bata shafi fadar ba, ana tsamanin wutar ta tashi ne sakamakon guntun karan sigari da wani mai wucewa ya jefar a kusa da wayar da ta zagaye ginin fadar.

“Da yammacin ranar Asabar 6 ga watan Maris, wuta ta tashi kuma ta ?ona yayi da ke tsakanin waya da kuma katangar da ta zagaye fadar Shugaban Kasa Villa, takamaimai tsakanin Villa da kuma Barracks da ke Asokoro,” in ji Garba Shehu.

Ya ce mutane da dama daga ciki da wajen Najeriya na ta bayyana damuwa game da rahoton gobarar, wanda ya ?ulla a wasu kafafen ya?a labarai.

Ya ?ara da cewa nan take dakarun kashe gobara suka kashe wutar, wadda ta fara kuma ta ?are a wajen ginin fadar.

Kazalika, ya ce ba a samu jikkata ko rasa rai ba kuma jami’ai na kan binciken musabbabin tashin wutar.

Related posts

Leave a Comment