Azabar Mulkin Tinubu: Duk Wanda Bai Ji Bari Ba Zai Ji Hoho – Mahdi Shehu

An bayyana wahala da jin jiki da Talakawa ke sha karkashin mulkin Shugaban ?asa Tinubu da cewar somin ta?i ce domin an jima da ankarar dasu masifar da za su fada amma suka yi biris.

Sanannen ?an kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahdi Shehu ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da suka yi da wakilinmu a Kaduna.

Mahdi Shehu wanda fitacccen magoyin baya ne ga ?an takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a za?en da ya gabata, yace talakawa dai sun ci taliyar karshe a wannan mulki saura kuma a hari gaba.

Dangane da batun shari’ar Atiku da Tinubu da yanzu ke gaban kotu kuwa Mahdi Shehu ya tabbatar Atiku zai yi nasara sai dai ya gargadi Alkalai da cewar su sani cewa duk iya shari’ar ka da akwai wanda ya fika kuma yana jira a madakata.

Related posts

Leave a Comment