Ayyuka A Ƙasa: Ku Matsawa Gwamnoni Ku Ƙyale Buhari – Fashola

Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, ya ja hankalin ƴan Nijeriya cewa su daina kallon dole Buhari ne zai magance kowace irin matsalar kasar nan, musamman matsalolin da jihohi ne su ka kamata su magance.

Ya ce ƴan Najeriya su na tsangwamar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ne saboda tunanin su gwamnatin sa ce za ta magance dukkan gagariman matsalolin da dokar kasa ta ce jihohi ne ke da alhakin magance su.

Ya ce dokar tsarin mulkin Najeriya bai dora wa gwamnatin tarayya wani nauyi mai yawan da ya kai na jihohi ba.

Saboda jama’a sun yi zaune turus kowa na jiran Gwamnatin Tarayya ko Shugaban Kasa ya yi masu aiki, shi ya sa su ke ta tsangwamar gwamnatin. To ina faɗa maku mu na neman a yi mana ayyuka ne, ba a inda ya dace mu nemi a yi mana ba.

Daga nan sai Fashola ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya cewa kowa ya je ya karanta Tsarin Dokokin Najeriya, domin ya ga yadda doka ta karkasa ayyukan gwamnatin tarayya, na jihohi da na kasanan hukumomi.

Ya ce idan su ka yi haka, to za su daina tunanin Buhari ne zai yi masu ayyukan da jiha ko karamar hukuma su ka cancanci yi masu ayyukan.

Labarai Makamanta