Aure Da?i: Hanan Buhari Ta Fitar Da Hotunan Bayan Aure

Wata daya bayan daurin aure, Hanan ?iyar Shugaban ?asa Buhari da Uwargidan shi Aisha Buhari, Amarya da Angonta sun saki sabbin hotunan bayan aure.

An daura musu aure a Masallacin fadar shugaban kasa ta Aso Villa A daurin aurensu, wanda manyan mutane a fadin Najeriya suka halarta, Amaryar da Angon sun samu albarkan iyaye da manyan malamai.

Amma an yi cece-kuce kan yadda aka gudanar da daurin auren. ‘Yan Najeriya da dama sun soki iyalan shugaban kasa a kan karya dokar babban bankin Najeriya (CBN) a wajen bikin Hanan Buhari, yadda aka yi ta liki da sabbin kudade ana rawa a kansu.

Sannan a yayin bikin Mutane da dama sun kuma yi fatali da dokar bayar da tazara a tsakanin jama’a wanda hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayar don hana yaduwar cutar Coronavirus.

Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da yan siyasa na ciki da wajen Najeriya wa?anda suka yi takanas domin shaida Auren.

Angon Hanan mai suna Muhammad Turad ?a ne ga Alhaji Mahmud Sani Sha’aban, tsohon dan majalisa wanda ya wakilci mazabar Zaria a majalisar wakilan tarayya daga Mayun 2003 zuwa 2007.

Hakazalika ya yi takaran kujeran gwamnan jihar karkashin jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN), kuma Basarake mai ri?e da Sarautar ?an Buram na Zazzau.

Related posts

Leave a Comment