Tsohon shugaban rundunar soji, Tukur Buratai, yace magajin sa, Ibrahim Attahiru, ya kama hanyar sanya Najeriya alfahari da ɗora ƙasar kan turba bayan lalubo bakin zaren warware matsalolin Najeriya da ya yi, sai dai kuma mutuwa ta yi mishi gaggawa inda ta ɗauke shi a daidai lokacin da Najeriya ke buƙatarsa.
Janar Buratai yace a fili yake marigayin ya ɗauko hanyar kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a ƙasar nan kafin wannan mummunan lamarin yayi sanadiyyar mutuwarsa, wanda dukkanin jama’a sun shaida hakan.
Ya bayyana hatsarin da abin tausayi ga yan Najeriya, yace Janar Attahiru da jami’an da suka rasu tare da shi sun bar tarihin da ba za’a taɓa mantawa dashi ba, a tarihin Najeriya har abada.
A cewarsa, hatsarin yayi matuƙar girgiza shi kamar yadda ya girgiza yan Najeriya saboda Attahiru ya mutu amma yabar mutane da yaƙinin irin nasarorin da ya samu a ɓangaren ayyukan soji.
Buratai yace:
“Attahiru ya kama hanyar sanya ƙasar mu alfahari bisa najimin ƙoƙarin da yake yi wajen magance matsalar tsaron da muke fama da ita, bani da tantama a kan ƙwazon shi saboda yayi aiki a ƙarƙashina a ɓangare daban-daban.”
“Nayi matuƙar kaɗuwa da baƙin cikin mutuwar Janar Ibrahim Attahiru, a hatsarin jirgin sama, wanda ya riƙe muƙamai da dama kafin zaman shi shugaban rundunar soji.”
“A madadin iyalaina ina miƙa saƙon ta’aziyya ga shugaban ƙasa Buhari, iyalan shi, ministan tsaro, jami’an sojin ƙasa da na sama bisa mutuwar waɗannan manyan jami’ai yayin da suke cikin aiki.”
Buratai ya roƙi hukumomin tsaro su tabbatar da ayyukan da waɗannan mutanen suka ɗauko bai tafi a banza ba, ta hanyar cika musu burinsu a ayyukan da suka fara.