Atiku Ya Dawo Najeriya Bayan Watanni Takwas A Dubai

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jami’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya dawo Najeriya bayan watanni 8 da yayi a Dubai.

Atiku ya sauka a filin jirgin Nnamdi Azikwe a daren Asabar bayan barin Najeriya tun watan Fabrairun na wannan shekara, mutanen da suka je tarbarsa basu da yawa, iyalansa ne da kuma abokan arzikinsa na kusa.

Wazirin na Adamawa ya dawo ne saboda cigaba da harkokinsa na siyasa, bayan barin kasar na wani lokaci.

Amintattun Atiku sun tabbatar da cewa, ba zai zauna ba har sai sun samu nasara a zaben gwamnan jihar Ondo dake tafe. Duk da majiyoyi daga iyalan Atiku sun ce, dawowar Atiku bata da wata alaka da siyasa.

Wani makusancin iyalan Atiku, wanda yace a boye sunansa, ya sanar da manema labarai cewa, Atiku ya dawo ne don yin ta’aziyya ga masarautar Zazzau saboda rasuwar sarki Alhaji Shehu Idris, sarkin Zazzau.
Tare da ta’aziyya ga Lamidon Adamawa, Dr Barkindo Mustapha, saboda rasuwar marigayiya Khadija Mustapha, wadda take matsayin kishiyar mahaifiyar sarkin, kuma mahaifiyar matar Atiku, Hajiya Rukaiya Atiku, da kuma iyalan Adamu Modibbo, wanda bai dade da rasuwa ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply