Rahotanni daga Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin dakatar da ACTED, wata ƙungiyar agaji ta Faransa mai zaman kanta da ake zargin tana bayar da horon harbin bindiga a wani otal a Maiduguri.
Sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar ranar Asabar ta ce ƙungiyar na gudanar da atisayen koya wa mutane harbi.
Gwamnatin Borno ta ce mutanen unguwar da ke kusa da otal ɗin ne suka bayar da rahoton cewa suna jin ƙarar harbin bindiga.
“Kuma bayan sanar da rundunar ƴan sanda da suka gano ginin otal ɗin, an samu ƙananan bindigogi na koyon harbi guda uku, mutum biyu da ake ba horo, dukkaninsu ƴan Najeriya suna hannun ƴan sanda ana bincike,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da ƴan sanda suka ƙaddamar da bincike, Gwamna Zulum ya bayar da umarnin rufe otal din tare da dakatar da ACTED daga duk wani aikin jin ƙai a jiharsa ta Borno