An bayyana cewar yankin Arewacin Najeriya na fuskantar barazana ta ?arkewar mummunan ya?in na kare dangi, sakamakon yadda al’amurra a kullum suke ?ara samun koma baya.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya suka fitar ?ar?ashin jagorancin Shugaban Gamayyar Nastura Ashir Sherif kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Kungiyoyin sun bayyana cewar halin da ‘yan Arewa ke ciki na kisa da musgunawa a ko’ina a fa?in kasar abin takaici ne.inda suka bada misalin da muggan kalamai da Gwamnan jihar Ogun ya yi na korar Fulani a yankin, da kisan gilla da ?an bangan nan Sunday Igboho ke yi akan jama’ar Arewa da barazanar Nnamdi Kanu a yankin Inyamurai.
Kungiyoyin sun kuma soki lamirin Gwamnatin tarayya karkashin shugaba Buhari na gaza yi wa tufkar hanci dalilin da ya haifar da Mummunan koma baya akai.
Kungiyoyin na Arewa sun kuma yaba ?o?arin da sanannen malamin nan Dr. Gumi ya ke yi na ganin an shawo kan matsalar ‘yan Bindiga a yankin arewa, inda suka nuna tasirin da goyon bayan shi.
Sannan a gefe guda sun soki dukkanin wa?anda ke sukar kokarin malamin na ganin an samu sulhu da lumana da ‘yan Bindigar inda suka bayyana masu wannan hali a matsayin miyagun masu amfana da matsalar tsaro da ake ciki.
Kungiyoyin Arewan sun kuma nuna goyon baya ga kudirin ?ungiyar Gwamnonin Arewa karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnati jihar Filato Simon Lalung na ho?basa da suke yi wajen shawo kan matsalar tsaro a Arewa.
Sannan sun yaba da matakan da kungiyar dillalan dabbobi da kayan Lambu suka ?auka na daina shigar da kayayyakin su yankin Kudancin kasar, har sai an kai ga biyan diyya na barnar da ?atagari suka yi ‘yan Arewa a yankin.
Kungiyar Arewan ta kuma yi kira da babbar Muryar ga gwamnatin tarayya bisa jagorancin Shugaban kasa Buhari, da yin dukkanin mai yiwuwa wajen ganin bayan wannan masifa da ke neman lashe yankin Arewa.