APC Ta Shirya Gagarumin Gangamin Karbar Gwamna Matawalle

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan jihar Bello Matawalle, zai tabbatar da komawarsa jam’iyyar APC a ranar Talata.

Saboda haka ne jam’iyyar ta shirya wani babban gangami na tarbar gwamna Matawalle zuwa APC wanda zai gudana a Trade Fair dake Gusau, babban birnin Zamfara da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar talata.

Ana sa ran jiga-jigan jam’iyyar APC na ƙasa da na jihar Zamfara ne zasu karɓi gwamnan, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Alhaji Ibrahim Dosara, yace ana sa ran aƙalla gwamnoni 18 ne zasu dira jihar Zamfara domin tarbar gwamna Matawalle.

Labarai Makamanta

Leave a Reply