APC Ce Za Ta Lashe Dukkanin Kujerun Kananan Hukumomin Kano – Ganduje

Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yi hasashen cewa jam’iyyarsa ta APC za ta lashe zaben dukkan kananan hukumomi 44 da gunduma-gunduma 484 dake jihar.

Ganduje ya ce ya yi hasashen haka ne bisa yadda ya ga mutane sun fito kwansu da kwarkwatansu domin kada kuri’arsu, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Yayin jawabi bayan kada kuri’arsa a kauyensa na Ganduje, ya ce an gudanar da zaben cikin zaman lafiya da lumana.

“Wannan na nuna cewa dukkan mutan jihar Kano sun amince da zaben,” Gwamna Ganduje ya bayyana haka.

Sai dai tun da fari babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kai ƙarar hukumar zaɓen jihar Kano Kotu inda take ƙalubalantar Hukumar da nuna rashin adalci a zaɓukan dake gudana da hada kai da jam’iyya mai mulki ta APC domin shirya maguɗi.

Rikicin siyasa a Jihar Kano dai ya kara zafi ne tun bayan kammala zaɓen Gwamna da aka yi a shekarar 2019, inda aka fafata tsakanin Gwamna Ganduje da Abbs Gida-Gida da ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Kwankwaso.

Labarai Makamanta

Leave a Reply