Hukumar ‘yan sanda ta ƙasa da ƙasa (Interpol) ta bayyana cewa ana wawure dubban daruruwan daloli daga Najeriya Zuwa Wasu kasashen Duniya a kowacce sa’a.
Wannan bayanin ya fito ne a Abuja ranar Litinin ta hannun mataimakin shugaban hukumar ‘yan sanda ta Interpol mai kula da Afrika, Garba Umar, yayin buɗe taron horar da jami’an tsaro na Najeriya na kwanaki hudu a makarantar horas da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
A cewar Garba Umar, safarar kudaden haram ta kai wani mataki mai ban tsoro a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya. Interpol ta gabatar da Sanarwa na Azurfa don magance wannan batu. “Shaidu sun nuna cewa dubban daruruwan daloli na fita daga Najeriya a kowace sa’a, ana karkatar da su kafin a kai ga masu aikata laifukan da ke cin gajiyar wannan haramtacciyar riba. A halin da ake ciki, ’yan Najeriya masu aiki tukuru da gaskiya sun dauki nauyin wadannan laifuka,” in ji Umar.
Ya kara da cewa samun nasarar halatta kudaden haram na kara wa kasar illar aikata laifuka da suka hada da safarar muggan kwayoyi, zamba, cin hanci da rashawa, da tashin hankali. “Kowace misali na cin nasarar haramun yana kara raunana cibiyoyin hada-hadar kudi,” in ji shi.