Ana Rainin Wayo A Najeriya – Falana

Fitaccen mai rajin kare hakkin bil adama kuma babban lauya a Najeriya, Femi Falana ya ce ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya daina raina wa yan kasar hankali da cewa akwai yiwuwar Amurka ta kawo dauki kan tabarbarewar tsaron kasar.

Falana cikin wata takarda da ya gabatar yayin taya Farfesa Omotoye Olorode, wani dan fafutuka murnar cikarsa shekara 80.

“Maimakon fadin abin da ba shi ne ba cewa Amurka za ta aika sojojinta domin kare su, ya kamata gwamnatin tarayya ta dukufa wajen daukar sojoji da yan sanda aiki ta ba su kayan aiki sannan ta ba su kwarin gwiwar samar da tsaro a kowane yanki na kasar,” in ji Falana a lokacin da yake gabatar da takardar a Abuja, babban birnin kasar.

Lauyan ya ce Amurka da kawayenta sun hana Najeriya samun mahimman kayan yaki saboda rahotannin take hakkokin bil adama da sojoji da yan sanda ke yi.”

“An zargi gwamnatin Najeriya da kin yin bayani kan ci gaba da tsare dubban mutane da sojoji ke yi ba tare da an kai su kotu ba da kuma irin cin zarafin da sojoji da yan sanda ke yi wa farar hula da basu ji ba su gani ba.”

Related posts

Leave a Comment