Ana Fargabar ‘Yan Bindiga Za Su Mayar Da Daruruwan Yaran Da Suka Sace ‘Yan Ta’adda

IMG 20240320 WA0010

Kungiyar Rajin Kare Haƙƙin Ƙananan Yara mai suna Child Protection Network, ta bayyana tsoro da fargabar cewa ‘yan ta’addar da suka sace ɗaruruwan yara ƙanana a Kaduna, Sokoto da Ekiti, za su iya yi masu tirenin su maida su ‘yan bindiga nan gaba.

Shugaban Ƙungiyar mai suna Kunle Sanni ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, a ranar Juma’a.

Sanni wanda ke zaune tare da sauran jami’an ƙungiyar, ya ce ya zama wajibi kare lafiya, rayuwa da samar da walwalar yara ƙanana su zama abu mafi muhimmanci da gwamnatin Najeriya ta za ƙara maida himma a kai.

Ya ce amma maganar gaskiya, a yanayi irin yadda mahara ke yawan sace ƙananan yara, to za fa ƙara samar da dandazon miliyoyin yara da ba su zuwa makaranta masu gararamba a garuruwa da yankunan karkara a faɗin ƙasar nan.

Ya bayyana cewa ya samu ƙwarai dangane da tsaron rayuka da lafiyar ƙananan yara, tare da yin kira a ƙara tsaurara matakan tsaro a dukkan wuraren da ake killace ƙananan yara, musamman a makarantu.

Sani ya tuna da ibtila’in sace ɗaruruwan yara sama da 200 a Jihar Kaduna, a ranar 7 ga Maris, sai kuma wasu da aka sace a Sokoto da Ekiti.

A kan yawaitar sace ƙananan yaran ne ya ce lamarin na ƙara nuni da cewa mummunan yanayi ne wannan ƙasa ta afka.

“Irin yadda ake arcewa da ɗaruruwan ƙananan yara ƙiriƙiri a tsawon shekaru a ƙasar nan, ya nuna gazawar gwamnati wajen kare rayukan su a makarantun ƙasar nan.

“Ana sace ɗalibai ba tare da samun tirjiya daga jami’an tsaro ba, duk kuwa da maƙudan kuɗaɗe har Naira biliyan 145 da aka ware don samar da tsaro a makarantun ƙananan yara. Wannan lamari abin damuwa ne, kuma ya yi muni. Kuma ya nuna gazawar ci gaban shirin katange makarantu, domin hana mahara afka masu.

“Kasa kare rayukan ƙananan yara a makarantu ba wai ilmi kaɗai zai kawo wa cikas ba, har ma da su kan su makomar yaran da kuma haifar da mummunan sakamako a cikin al’umma nan gaba.” Inji Sanni.

Labarai Makamanta

Leave a Reply