Ana Cuwa-Cuwa Wajen Tallafin Dubu 20-20 A Kaduna

Wasu mata a jihar Kaduna sun koka kan zargin sama-da-fadi da son kai a cikin tallafin N20,000 da ke gudana wanda Ma’aikatar Kula da Jin Kai ta Tarayya ke yi a jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ana tsananin yin cuwa-cuwa da sama da fadi akan ku?in tallafin wanda aka ware domin talakawa, amma sai wasu manyan Mata a jihar ke cigaba da amfana.

An ruwaito cewa mutanen da ba a san su ba suna karbar kudade daga wasu daga cikin wadanda suka amfana. Sun yi zargin cewa akwai akasarin wadanda aka yi niyyar su ci gajiyar shirin kamar yadda aka tsara, inda suka kara da cewa wadanda suka amfana “galibi dangi ne da abokai na jami’ai da ‘yan siyasa.’’

?aya daga cikin matan, Khadija Ahmad, ta shaida wa NAN cewa tallafin da aka tsara don bayar da hannun jari ga wasu ‘yan kasa masu fama da talauci da masu rauni suna karewa a aljihun wasu.

A cewar ta, wasu daga cikin matan da suka ci gajiyar sun tuko mota zuwa wurin a cikin motoci masu wal?iya da ke nuna alamar cewa ba sa bu?atar irin wannan tallafi.

Wata mata mai suna Malama Rabi Mohammed ta ce an tattara sunayen kusan 50 daga cikinsu an ce su zo wurin taron a kungiyance, tana mai kuka cewa babu wani daga cikinsu da ya karbi kudin.

“Mun kasance muna zuwa nan kowace rana tsawon kwanaki uku da suka gabata, tare da wasun mu suna zuwa da misalin karfe 6:00 na safe amma basu sami komai ba.

“Mun kuma ga an ba mutane biyar N20,000 su raba, maimakon N20,000 kowane, yayin da wasu da aka taimaka suka raba tsakanin N15,000 zuwa N17,000 ga mutanen da suka taimaka musu.”

Related posts

Leave a Comment