Ana Cigaba Da Tsare Matashin Da Ya Yi Barazanar Harbe Buhari

Solomon Akuma mahaifin wani matashi da ke aiki da hukumar NAFDAC, Emmanuel Akuma, ya bada labarin yadda ?an sa ya shiga hannun ‘yan sanda bayan wani rubutu da ya yi a shafin sada zumunta na barazanar sa wa a kashe Buhari.

Solomon Akuma wanda Fasto ne a Cocin Truevine Evangelical Mission da ke Delta, ya ce dakarun FCID sun cafke masa yaro, kuma har kawo ya zuwa wannan lokaci bai san halin da ?an nashi yake ciki ba.

Solomon Akuma ya shaidawa manema labarai cewa tun watan Afrilun 2020, ‘yan sanda suka kama Emmanuel Akuma mai shekaru 29 a garin Aba, jihar Abia bisa ga wasu dalilai da suka bayar.

Matashin ya zo shafin Twitter yana cewa zai biya ‘yan bindigan kasar Rasha kudi domin su harbe shugaban kasa (Buhari) da Marigayi shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban Kasa Abba Kyari.

Akuma ya yi wannan ganganci ne bayan wani ya jefa tambaya a shafin twitter, ya na tambayar mutane abin da za su yi idan suka samu dala miliyan $1m.

Mahaifin wannan yaro ya ce: “Da ni su ka yi amfani suka kama yarona. Sun bincika sun gano ni fasto ne.” A haka ‘yan sanda su kayi masa tarko, suka kama shi.
“Wani ya kira ni ya fada mani cewa na taba yi masa addu’a, ya ce yana so ya karrama ni tare da wasu, ya fada mani lokacin da zai zo.” Sai ga Akuma a hannun FCID.

Daga nan jami’an tsaron su ka yi nasarar cafke matashin, su ka tsare shi a Abuja. Bayan wata uku aka gurfanar da shi a kotu bisa zargin aikata wasu tarin laifuffuka marasa adadi.

Tun shekarar 2017 Akuma ya yi wannan barambarama, amma yanzu watanni tara kenan ana cigaba da tsare shi.

Related posts

Leave a Comment