Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

An Zo Wajen.. Garin Kwaki Na Neman Gagarar Talaka

images (83)

Farashin garin kwaki ya ?aru da kashi 50 bisa 100 a garin Enugu, jihar da ake sarrafa shi hai?an, kuma ana ganin a irin can ne ma ya kamata a ce an samu sau?in farashi.

Yayin da garin kwakin wanda ake wa kallon cimar talakawa ne ya ?ara tsadar da ya ke neman ya gagari, talakawan, ita ma shinkafa ta ?ara tsadar da idan ka saya kwana biyu baya, muddin ka koma kasuwa a yau, to idan ka ji farashin, sai dai ka koma gina ka sake dabara, ko ‘yan dabaru.

Binciken da aka yi a garin Enugu ya nuna cewa yawancin wa?anda ke sayen mudu-mudu a baya, yanzu lamarin ya gagare su, sun koma sayen kofi-kofi.

Lita 5 na garin kwaki, wato cikin bokitin fenti ?aya, wanda a cikin Janairu ake sayarwa Naira 2,000 zuwa Naira 2,200, to daga ranar Lahadi da ta gabata ya koma Naira 2,700.

Su ma marasa galihun da ba su iya sayen mudun garin kwaki, ?an kofi ?aya ko kofi biyun da suke saye a yanzu ya tashi zuwa Naira 150 duk kofi ?aya, har Naira 200.

Yayin da wakilin mu a Kano ya ji wani ya na cewa, “Ni dai gara na sayi kofin garin rogo Naira 200 da a ce na bayar da Naira 400 a ba ni Indomi guda ?aya. Idan teburin mai shayi na je, sai na bada Naira 500 za a dafa min Indomi ?aya. Wannan rayuwa ya ake so mu yi ne?”

Wata mata mai suna Bridget Ugwu da ke sayar da garri a Sabuwar Kasuwar Enugu, ta ce hanya ?aya da za a sauko da farashin gari ita ce a fa?a?a noman rogo ta hanyar ?ara share dazuzzuka, domin a samu wadatar gonaki. Sannan kuma a daina fitar da shi kasashen da ke ma?autaka da mu.

Ita kuwa Ochuba Ozor da ke sayar da shinkafa, ta ce a yanzu sai ta ?auki lokaci mai tsawo ba a sayi shinkafa ba a rana. Ta ce amma kafin ta yi tsada, har tururuwa ake yi ana layin saye a wurin ta.

Tuni dai talakawa suka fara tare manyan motocin dakon kayan abinci su na daka wasoso a garuruwa daban-daban a fa?in ?asar nan.

Exit mobile version