An Zartar Da Hukunci Akan ‘Yan Boko Haram Shida

Wata babbar kotun kasar hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta zartar da hukunci a kan wasu ‘yan Najeriya shidda kan laifin taimakawa kungiyar ‘Yan ta’addan boko haram da kudade masu yawa. Ana zargin mutanen da yin amfani da kudadensu wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram inda kotun ta yankewa biyu daga cikinsu hukuncin daurin rai da rai a gidan yari, sauran hudun kuma daurin shekara goma kamar yadda jaridar daily trust ta wallafa.

Biyu daga cikin waɗanda ake zargin, Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf an yanke musu hukuncin zaman gidan yari iya tsawon rayuwarsu. Su kuwa sauran mutane huɗun da suka haɗar da; Ibrahim Ali Alhassan, AbdurRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf, da Muhammad Ibrahim Isa, dukkansu an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara goma.

Jaridar Daily trust ta gano cewar ana tuhumar masu laifin ne tun shekarar 2019 inda aka gano daga shekarar 2015 zuwa 2016, wadanda ake zargin sun tura zunzurutun kudade har Dala $782,000 zuwa kungiyar Boko Haram, sai dai makusantan wadanda ake zargin sun ce an tura kudin ne a bisa halal ba don daukan nauyin ayyukan ta’addanci ba.

Sama da shekaru 11 da suka gabata, ana fama da rudani da zarge zarge akan masu d’aukar nauyin k’ungiyar. Wannan shine karo na farko da aka gano masu aikata hakan a wajen Najeriya.

Wani babban jami’in gwamnatin Najeriya yace suna da masaniya akan shariar . Har yanzu gwamnatin tarayya ba ta sanar da sunaye balle ta zartar da hukunci a kan ma su daukar nauyin kungiyar Boko haram ba duk da rundunar soji ta sha ikirarin cewa sun san ma su yin hakan.

Kuna ganin wannan hukuncin ya dace ko kuwa akwai abinda ya kamata ace gwamnatin Najeriya tayi akan wa’innan mutanen?

Labarai Makamanta