Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kwamitin da ke sa ido kan harkokin majalisar dattijan Najeriya ya yi korafi a kan yadda shugabannin majalisar ke nuna rashin adalci wajen jagoranci.
Sanata Garba Musa Maidoki na PDP daga jihar Kebbi, ya shaida wa BBC cewa a yanzu ya lashi takobin fafutikar ganin an inganta yadda ayyukan Majalisar ke kasancewa domin ciyar da kasa gaba.
Sanata mai doki ya ce lokaci da ya yi da wajibi a sanya bukatun al’umma kan gaba, maimakon yadda yawancin yan majalisar ke fifita bukatunsu.