Al’ummar Tarauni a jihar Kano karkashin kungiyar cigaban Darmanawa Layout, na zargin asusun lamunin birnin Ado Bayero, wani asusun masarautar Kano, da yunkurin kwace filin Idi da kuma sayar da shi.
Shugaban kwamitin filin Idi, Barista Tijjani Yahaya, ya bayyanawa manema labarai a jihar Kano cewa marigayi Ado Bayero ne ya bayar da filin kyauta ga garin kuma gwamnatin jihar ta tabbatar da hakan.
Tijjani Yahaya ya bayyana cewa irin haka ya taba faruwa a 2019 lokacin da wasu sukayi kokarin sayar da filin. A cewarsa, Filin shine wajen Sallan idi daya tilo dake karamar hukumar Tarauni gaba daya.
Shugaban kungiyar ya kara da cewa sun rubuta wasika ga hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa na jihar Kano a Oktoban 2020, domin hana masarautar kwace filin.
“Yayinda muke sauraron sakamakon wadannan kararraki da muka shigar, wakilan asusun lamunin birnin Ado Bayero sun yi kokarin kwace filin karfi da yaji kuma mun samu nasaran hanasu a 30 ga Disamban, 2020.”
“Saboda haka, muna kira ga asusun lamunin Ado Bayero ya gabatar da wata hujja dake nuna cewa filinta ne.”
Har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton dai ɓangaren masarautar Kano ba ta yi martani akan wannan zargi da ake yi mata ba na sayar da filin idi.