An Zargi Gowon Da Wawushe Ku?a?en Najeriya Lokacin Barin Mulki

Wani ?an majalisar kasar Birtaniya, ya fito ya na ikirarin cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Yakubu Gowon, ya saci kudin al’ummarsa fiye da yadda ake tunani a yayin ban kwana da Kujerar Shugabancin kasa a shekarar 1976.

?an majalisar ya bayyana wannan ne a gaban wani zaure, inda ya jefi Janar Yakubu Gowon mai ritaya da laifin awon gaba da rabin kudin babban bankin Najeriya a wancan lokaci CBN.

Ya ?ara da cewar “Mun san yadda Janar Yakubu Gowon ya yi awon-gaba da rabin dukiyar da ke cikin babban bankin Najeriya (CBN), ya tsere Landan.”

?ann Majalisar bai kawo wasu hujjoji da za su gamsar da abin da ya yi da’awa ba, ya nuna rade-radi ya samu, ya ce: “Kamar yadda ake fada.”

Sannan ya cigaba da cewa: “Mun san cewa a cikin birnin nan namu, abin ban haushi, akwai wasu dasu ka lamushe kudin mutanen Najeriya da aka sace.” “Mun san ana amfani da bankunanmu wajen wannan aiki (wawuran dukiyar sata), don haka Ingila na da damar huro wuta a kan masu sace kudin Najeriya.”

Duk da cewa Najeriya ta samu makudan kudi a lokacin da Janar Yakubu Gowon ya yi mulki tsakanin 1966 – 1975, babu hujjar ya yi sata daga babban bankin ?asa CBN.

A lokacin da aka kifar da Gowon daga mulki ya na Uganda, kuma daga nan ya zarce zuwa Ingila, amma ba a zarge shi da satar kudin bankin CBN ba.

A ranar 19 ga watan Oktoba, 2020, Janar Yakubu Gowon ya cika shekara 86 da haihuwa. Gowon ya yi karatu a makarantar sojoji ta Royal Military Academy Sandhurst, Ingila, Staff College, Camberley, da kuma Joint Staff College a garin Latime.

Related posts

Leave a Comment