An Yi Saukar Kur’ani Da Addu’o’i Miliyan 41 Domin Ganin Bayan Boko Haram A Maiduguri

Mutanen Borno sun yi addu’oi sama da miliyan 41 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya domin neman kawo ?arshen masifar da mayakan kungiyar Boko Haram suka jefa su a ciki.

Wata ?ungiya ce mai suna Borno Concerned Citizen wato ?an jihar da suka damu da halin da take ciki ta jagoranci taron addu’o’in a ranar Lahadi.

Barista Zahra Maiduguri ?aya daga cikin wa?anda suka jagoranci addu’o’in ta bayyana wa BBC Hausa cewa an yi saukar Al ?ur’ani da kuma addu’oi 41, 837,016 domin neman sau?in masifar da jihar take ciki.

Daga cikin addu’o’in har da “Istigifari” miliyan 13,669,000 da “Ya La?ifu” miliyan 10,688,00.

An kuma yi “Ya Kahharu” fiye da miliyan ?aya da salatin Annabi da kuma salatil fati.

Baya ga addu’u’oin an kuma yanka dabbobin shanu da nufin yin sadaka domin Allah ya biya bu?ata.

?ungiyar ta kunshi shugabanni na siyasa da na gargajiya da malaman addini da malaman Boko a jihar Borno.

Mayakan Boko Haram sun kwashe fiye da shekara goma suna kai hare-hare a arewacin Najeriya, musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Hare-haren sun yi sanadin mutuwar dubban mutane da kana suka raba miliyoyin jama’a da gidajensu.

Harin Zabarmari inda ?ungiyar ta yi wa manoma yankan rago shi ne hari na baya-bayan nan mafi muni da Boko Haram ta kai a jihar Borno.

Related posts

Leave a Comment