Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

An Yi Mini Tayin Miliyan 150 Da Motar Miliyan 80 Domin Na Bar Atiku – Sarkin Waka

Fitaccen jarumin Kannywood, Naziru Ahmad, da aka fi sani da Sarkin Waka ya yi ikirarin cewa an bashi Naira miliyan 150 da mota ta naira miliyan 80 don ya yi watsi da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, gabanin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu amma ya ƙi.

Naziru Ahmad na daya daga cikin mawakan Hausa wadanda suka yi wa Atiku wakoki na kamfen kuma ya yi wasa a wurin ralli na jihohin arewa 19.

Da ya ke magana a wani shirin DW Hausa, mawakin na Kannywood ya ce ya ki amincewa ya yi watsi da Atiku don goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu.

Naziru Sarkin waka ya ce ya yi imanin cewa Atiku ya fi Tinubu lafiya don haka zai fi shi tabuka abin azo a gani idan ya ci zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

“Na fifita maslahar kasa fiye da bukatar kashin kai na. “An bukaci in bar tafiyar Atiku domin wani dan takara kuma za a biya ni Naira miliyan 150 tare da mota ta Naira miliyan 80 amma ban karba ba. “Na ki amincewa da tayin saboda na san Atiku zai yi shugabanci na gari kuma zai tsamo Najeriya daga mummunan halin da ta ke ciki.

“Ta yaya zan goyi bayan Tinubu wanda ba shi da lafiya da kwarin jiki? Addinin mu ya koyar da mu mu zabi masu lafiya a matsayin shugabanni don yana daya cikin halayen shugaba na gari.”

Exit mobile version