An Yi Bikin Cikar Marigayi Dan Kwairo Shekaru 30 Da Rasuwa


Shahararren mawakin nan a kasar Hausa, marigayi Alhaji Musa Dan kwairo ya cika shekara 30 da rasuwa.

Dankwario na daya daga cikin mawakan Hausa da ya yi ficen da ya zarta mawaka a zamaninsa a wakokin fada ko sarakai.

Duk da tsawon lokacin da aka yi da rasuwar mawakin, har yanzu masoya wakokinsa na ci gaba da kewarsa, kan haka ne Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya ta shirya wani taro tare da hadin gwiwa da Sashen Nazarin harsunan Najeriya da kuma sashen Nazarin kimiyyar harshe na jami`ar Bayero ta Kano.

Related posts

Leave a Comment