An Yanke Wutar Marigayi Shehu Shagari

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki reshen Kaduna (KEADCO) ya yanke wutar gidan shugaban Nijeriya a jamhuriyya ta biyu marigayi Shehu Shagari da ke Sokoto, kan rashin biyan kudaden wuta da suke bi har kimanin sama da Naira miliyan shida.

Marigayi Alhaji Shehu Shagari ya rasu ne a ranar 28 ga Disambar shekarar 2018 yana da shekaru 93 a duniya.

Da ya ke tabbatar da yanke wutar, ga jaridar DAILY NIGERIAN, kakakin kamfanin, Abdulaziz Abdullahi, yace bayan rasuwar Shagarin ne aka daina biyan kudin wutar gidan.

“Kuma kamfanin ya ba iyalan marigayin isasshen lokaci su ci gaba da biyan kudaden kafin yankewar,” in ji Abdullahi.

Wata majiya daga ahalin marigayin tace kafin mutuwar Shagari, gwamnatin jihar Kaduna ce ke biyan kudin wutar lantarkin tsohon shugaban.

Wani jami’in gwamnatin Sokoto da ya nemi a sakaya sunansa, yace bai kamata a zargi gwamnatin jihar Sokoto ba, sai dai gwamnatin tarayya ce taki biyan kudin wutar gidan marigayin.

Labarai Makamanta