An Wayi Gari Da Ganin Hotunan Sunusi Lamido A Fadar Gwamnatin Kano

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewa an wayi gari an ga an daura hotunan Muhammadu Sanusi II da na Shugaban kasa da Gwamna a gidan Gwamnatin jihar Kano.

Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tunbuke Sanusi II daga sarautar Kano bayan an yi zaben 2019 Ana rade-radin Basaraken zai sake rike sarautar idan Jam’iyyar NNPP ta kafa gwamnati a Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa an hangi hotunan Sarkin Kano na 14, Mai martaba Muhammadu Sanusi II a gidan gwamnatin jihar Kano. Wani ‘dan kasuwa mai suna Kabiru Garba ya daura wannan hoto a shafin Facebook a ranar Lahadi. Injiniya Kabiru Garba da ya fito da abin sarari ya kyankyasa cewa Muhammadu Sanusi II zai dawo kan karagar mulkin da ya bari a 2019.

Da yake tsokaci akai daya daga cikin ‘ya’yan tsohon Sarkin mai suna Ashraf Sanusi ya bayyana cewa Wannan ya zama jan-kunnen karshe ga makiyan Muhammad Sanusi II. Dubi yadda abubuwa za su kare, ba sa’anku ba ne.”

Related posts

Leave a Comment