An Shiga Zawarcin Neman Kujerar Shugaban Dakarun Soji

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tuni wasu manyan Hafsoshin Soja masu mu?amin Janar suka shiga harin neman kujerar shugaban Dakarun sojojin Najeriya, hakan na zuwa ne bayan mutuwar Laftanan-Janar Ibrahim Attahiru a ranar Juma’a.

An ruwaito cewar rade-radin da ke yawo na nada Manjo-Janar Danjuma Ali-Keffi a matsayin sabon Shugaban Dakarun sojan kasan Najeriya, ba gaskiya ba ne bai inganta ba, asali ma akwai manyan sojojin kasa fiye da 30 a gaban Manjo-Janar Danjuma Ali-Keffi a yanzu.

A zahiri, akwai manyan jami’ai sama da 30 da ke sama dashi. Saboda haka, wani babban hafsan soji ya bayyana cewa ana la’akari da dalilai da yawa wajen nadin shugabannin rundunoni da manya a gidan soja. “Kun san Shugaban kasa yana da ikon nada duk wanda yake so tare da shawara ko wata kila daga Ministan Tsaro.”

Jami’in ya ce “Baya ga girman mukamai a cikin aikin, jami’an da ake yin la’akari da su tabbas su kasance suna cikin ayyukan soja da leken asiri.

Daga rahoton na PRNigeria, ga jerin manyan jami’an da ake sa ran daya daga cikinsu watakila ya maye gurbin marigayin kasancewarsu manyan jami’an rundunar soji.

1. Manjo Janar Ben Ahanotu daga jihar Anambra Shi ne Kwamandan rundunar Sojoji da suka kame wanda ya kafa kungiyar Boko Haram Mohammed Yusuf da mabiyansa a maboyarsu a Maiduguri a shekarar 2009 kuma ya mika su ga ’yan sanda.

2. Manjo Janar AM Aliyu daga jihar Gombe Shi ma wani babban jami’i ne. Shi ne Shugaban Gudanarwa na Sojojin Najeriya kuma tsohon Daraktan hulda da kasashen waje a Hukumar Leken Asiri ta Tsaro. Ya kasance mai alhakin sarrafa bayanan sirri na ayyukan soja.

3. Manjo Janar Ibrahim Manu Yusuf daga jihar Yobe Shi ne Babban Jami’in Tsaro kuma tsohon Kwamandan Rundunar Soja na Hadin gwiwa ta Multinational Joint Taskforce (MNJTF). Ya kuma kasance tsohon Kwamandan Operation Lafiya Dole tare da gogewa a fagen yaki da ta’addanci da ayyukan tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas. Ya kuma koyar a kwalejojin soja da yawa ciki har da NDC, NDA da sauransu.

4. Manjo Janar Faruk Yahaya daga jihar Zamfara Shi ne kwamandan yaki a yanzu a Arewa maso Gabas kuma tsohon Babban Kwamandan Runduna ta 1 na Sojojin Najeriya.

Related posts

Leave a Comment