An Shiga Taraddadi Akan Na?in Sabon Shugaban ‘Yan Sanda

Rashin tabbas sun mamaye rundunar Yan Sandan Najeriya, sakamakon kawo karshen wa’adin aikin Sufeto Janar Muhammadu Adamu daga wannan Litinin, amma kuma ya zuwa yanzu shegaban kasa Muhammadu Buhari yaki cewa komai kan lamarin.

Bisa ka’idar aikin gwamnati, gobe Sufeto Janar Adamu ke cika shekaru 35 a cikin aikin gwamnati, abinda ya zama masa wajibi ya tafi ritaya.

Rahotanni sun ce Adamu ya bukaci karin lokaci domin cigaba da aiki har sai ya cika shekaru 60 amma fadar shugaban kasa bata ce komai ba kan bukatar.

Bayan shi Sufeto Janar din, akwai wasu mataimakan sa da suma suka kawo wa’adin aikin su, kuma ake saran su tube kakin su daga Litinin din nan.

Kamar yadda aka saba, shugaban kasa kan nada wanda zai gaji Sufeto Janar kafin ranar kammala wa’adin mulkin sa, yayin da Majalisar koli da ta kunshi Gwamnoni da tsoffin shugabannnin kasa da tsoffin manyan alkalan kasa da mai rike da kujerar yanzu da shugabannin Majalisa na da da na yanzu zasu zauna su amince da nadin.

Ya zuwa lokacin wallafa wannan labari, babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, yayin da ake cigaba da shaci fadi kan makomar Sufeto Janar din da kuma wanda ake saran ya gaje shi.

Related posts

Leave a Comment