Tun bayan bayanan da tayi a kwanakin baya na barazanar kashe kanta saboda kuncin rayuwa, tsohuwar jarumar Finafinan Hausa Ummi Zee-Zee na cigaba da fuskantar suka a ?angarori da dama.
Wanda ya fi kowa sukar tsohuwar jarumar a masana’antar Kannywood shine fitaccen jarumin nan Zaharadeen Sani, inda ya fitar da wasu bayanai na ba’a ga jarumar.
Alamu sun nuna Ummi Zee-Zee bata ji dadin kalaman jarumin ba, hakan ya sanya ta fitar da wani bidiyo tana shagube a gareshi inda take fa?in cewa ta fi karfin jarumin kuma har ya mutu ba zai yi arziki kamar ta ba.
Ummi Zee-Zee ta bayyana Zaharadeen Sani a matsayin ?an wiwi mara manufa wanda talauci ya sanya shi auren almajira ‘yar sadaka yalla.
Sai dai tun da fari sai da Jarumi Zaharadeen Sani ya bayyana Ummi Zee-Zee a matsayin wadda ke fama da matsalar tabin hankali bisa ga haka bai da lokacin ta.