An Shiga Cacar Baki Tsakanin Shugaban ‘Yan Sanda Da Tsohon Janar

Babban Baturen rundunar ?ansanda na ?asa, IGP Mohammed Adamu, ya maida martani ga wani tsohon janaral ?in soja, Garba Wahab, mai ritaya, wanda ya zarge shi da rashin kula da ragamar rundunar ?ansanda yadda ya kamata.

A wani jawabin maida martani da mai magana da yawun rundunar ?ansanda, DCP Frank Mba, ya sawa hannu kuma ya rabawa manema labarai, Shugaban ‘Yan Sandan ya yi watsi da kalaman Wahab, inda yace kalamansa ba dai-dai bane domin kuwa yana kula da ragamar rundunar yadda ya kamata.

Yace Wahab yayi magana cikin rashin sani da kuma rashin fahimtar ayyukan ?ansanda a mulkin siyasa na dimokara?iyya.

“Rundunar tana sanar da Manjo Janaral mai ritaya cewar ya sa?a lamba bisa kalaman da ya yi akan babban Shugaban rundunar ?ansanda na ?asa.

“Janaral Wahab ya yi kalaman ne cikin ?ungurmin jahilci da rashin fahimtar yadda ake tafiyar da ayyuka da kuma al’ada irin ta aikin ?ansanda a dokance.

Tsohon Sojan mai ritaya ya yi magana akan sha’anin da baida masaniya akai, tunda ba huruminsa bane ba. “Sanin kanmu ne cewar tun bayan da ya zama Babban Shugaban ?ansanda, IGP Mohammed Abubakar Adamu, NPM, mni,?ansanda ne abin koyi a duniya.

“A watanni uku da suka gabata tun bayan fara jan ragamar rundunar, ya nuna ?warewa a fannonin atisaye da kuma nuna misalin a kan yadda jami’ai zasu kasance”.
“Zaku iya ganin misalai daga yadda ya ke ?o?arin kawo sauye – sauye don inganta ayyukansu, da kuma ?abba?a doka a ayyukan ?ansanda, baya ga ?o?arin inganta mu’amalarsu da mutane da kuma kare ha??in ?an?asa.

“Tabbas ya yi abin a yaba masa musamman lokacin zanga-zangar #EndSARS, duba da yadda jami’ai suka jure hare-hare da hargitsi gami da lalata dukiyoyi ba tare da sun salwantar da rayuwar kowa ba.
“Irin Wannan salo nashi ya nuna ?warewarsa da kuma kuma biyayya ga doka da tsarin ?asar.

“Rundunar ta shawarci jama’a da kada su bari wasu su sauya musu ra’ayi da zancen shifcin gizo.Ta kuma shawarci masu sukar ayyukan hukumar da suke taimaka mata da shawarwarin da zasu inganta tsaro a ?asar.

Da fatan Manjo janaral Garba Wahab zai ringa nazarin magana kafin ya furta jama’a su ji”

Related posts

Leave a Comment