Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

An Shawarci Tinubu Ya Yi Amfani Da Karfin Iko Wajen Kafa ‘Yan Sandan Jihohi

IMG 20240226 WA0252

Kungiyar kishin kabilar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya da ya yi amfani da ikonsa ya bayar da umarnin kafa rundunar ‘yansandan jihohi da ta kananan hukumomi.

Sakataren yada labarai na kungiyar, Jare Ajayi, ne ya fitar da sanarwar da ke dauke da kiran yau Asabar, a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce, kungiyar ta yi kiran ne sakamakon rahotannin da ake ta samu na karin hare-haren ‘yan bindiga da satar jama’a a jihohin Ogun da Edo da Ekiti da Oyo da Kogi da Zamfara da kuma Naija, abin da har wata kungiya mai bincike ta ayyana Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashe da aka fi satar mutane a duniya.

Kungiyar ta ce ya zama wajibi Shugaba Tinubu ya tabbatar da kafa rundunonin ‘yansandan jihohi da na kananan hukumomi ba tare da bata wani lokaci ba, ta hanyar bayar da umarni, yayin ake ci gaba da aikin yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima.

Haka kuma kungiyar ta Yarabawa ta yi kira da a kakkafa na’urorin daukar hoto na tsaro da sauran kayayyakin fasaha na tabbatar da tsaro a muhimman wurare domin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar.

Exit mobile version