An Shawarci Tinubu Ya Binciki Tsohon Sarkin Kano Sanusi

An shawarci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya fadada binciken da ke gudana a ofishin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele har zuwa zamanin Sanusi Lamido. Kimanin shekaru tara kenan da sanusi ya rike mukamin gwamnan babban bankin Najeriya har zuwa lokacin da aka sauke shi a 2014

Shugaban kungiyar goyon bayan Tinubu kuma Darakta Janar na kungiyoyin hadaka na APC, Mista Kailani Muhammad ne ya bayar da shawarar, a wata tattaunawa da manema labarai a Kaduna.

Kailani ya lissafa matsalolin da suka yi sanadiyar tsige Sanusi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi a 2014, yana mai cewa bai kamata Tinubu ya yi watsi da lamarin ba.

Kailani Muhammad ya bukaci shugaban kasa Tinubu da kada ya damu da ziyarar da tsohon sarkin Kanon ya kai masa, yana mai bayyana su a matsayin dabarun neman jan hankali. “Muna ta ganin tsohon gwamnan CBN, Sanusi Lamido, kusa da fadar shugaban kasa da sauran wuraren gwamnati kuma wannan ne tushen damuwarmu. Muna so mu ba da shawarar cewa kada shugaban kasa ya saurare shi.

“A zahirin gaskiya, muna so a fadada bincike zuwa zamaninsa a matsayin tsohon gwamnan CBN. Akwai batutuwa da dama a wuyansa wanda ya sa tsohon shugaban kasa Jonathan ya dakatar da shi.

“Mun san cewa Emefiele yaronsa ne. Ya kamata shugaban kasa ya bincike shi tare da Emefiele don su fito da kudinmu saboda dalilai na ci gaba.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply