An Samu Sa Hannun Magu A Badakalar Maina

A cigaba da zaman Shari’a da ake yi na tsohon Shugaban Hukumar Fansho Abdulrasheed Maina dangane da tarin zargi da ake yi masa na yin sama da fadi da dukiyar jama’a, wasu shaidu sun bayyana cewar an samu hannun tsohon shugaban EFCC Ibrahim Magu cikin badaƙalar.

Wani jami’in hukumar ta EFCC Ngozika Ihuoma, wanda ya bada shaida a kotu a ranar Alhamis, ya jefa tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu, a badakalar ta Abdulrasheed Maina.

Ana shari’a a kotu inda ake zargin tsohon shugaban kwamitin binciken kudin fansho (PRTT), Abdulrasheed Maina da yin sama da fadi da dukiyar al’umma. Ngozika Ihuoma ya sanar da Alkalin kotu, Okon Abang, yadda wani jami’in EFCC ya mallaki wani gida da ake bincike a kai, yayin da ake tsakiyar zaman shari’ar a kotu.

Wanda ya bada shaidan ya nemi EFCC ta fito da kadarori 222, daga ciki har da wani katafaren gidan Biliyan 6 da aka saida wa Lauyan EFCC a kan Biliyan 1 rak zamanin Shugabancin Magu.

Mista Ihuoma ya ce a lokacin da Magu ya bayyana a gaban majalisar wakilai a kan binciken dawo da Maina bakin aiki, ya musanta cewa PRTT ta na tare da hukumar EFCC. Sannan shaidan ya bayyana cewa Magu ya yi ikirarin PRTT ba ta mallaka wa EFCC wasu kadarori ba.

A dalilin hakan, wannan mutumi da yake bada shaida ya sanar da kotu cewa Ibrahim Magu ya yi karya, ya kuma karya rantsuwar da a yi a binciken Maina da aka yi.

Lauyan da ya ya tsaya wa tsohon shugaban PRTT da aka ruguza, Olawale, ya shaida wa kotu yadda Maina ya fada wa gwamnati hanyar da za ta karbo Naira tiriliyan 3.

Adeola Olawale ya ce a 2016 Maina ya hadu da NSA da AGF a Dubai, ya yi masu bayanin yadda za a bi a karbo N1.3tr daga cikin N3tr da aka wawura daga baitul-mali.

Kwanakin baya ne Jami’an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci su ka kama Abdulrasheed Maina a Nijar, bayan ya sulale daga Najeriya. An samu nasarar kama Maina ne saboda kyakyawar alakar da ke tsakanin jami’an Najeriya da Nijar.

Da ake zaman kotu, Abdulrasheed Maina ya ce bai aikata laifin komai ba duk da cewa hukumar EFCC ta na yi masa tuhuma 12, kuma ya tsere bayan ya samu beli.

Labarai Makamanta

Leave a Reply