Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban bankin ƙasa CBN ya ce kasar ta samu ribar Naira biliyan 799.10 a bangaren albarkatun man fetur a rubu’in farko na shekarar 2022.
Alkaluman sun nuna raguwar ribar da kashi 28.3 cikin dari, idan aka kwatanta da ribar tiriliyan 1.11 da aka samu a rubu’in karshe na shekarar 2021.
An ruwaito daga majiya mai tushe cewa kuɗin tallafin da kasar ta biya a rubu’in farkon ya kai biliyan 675.
Ribar man fetur din dai ya hadar da ribar danyen man fetur da iskar gas da aka fitar zuwa kasuwannin duniya, da kuma wanda aka sayar a cikin kasar