An Samu Hatsarin Jiragen Sama A Legas

Wasu jirage biyu mallakin kasashen waje sun yi hadari a babbar tashar sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Murtala Muhammad International Airport dake birnin Lagos.

Jirgin kamfanin Sufurin Meddle East Airlines ne ya yi bugi na Turkish Airlines wanda yake tsaye har aka balle masa bindi.

Wani ganau ya shaidawa wakilinmu cewa, jirgin Middle East ne ya gwara na kasar Turkiyya a yayin da yake kokarin tashi.

Ganau ɗin ya bayyana cewa, “lamarin ya faru ne a yayin da jirgin Middle East ke kokarin tashi bayan ya kwashi fasinjoji tun karfe 12 na rana”.

Yanzu dai faruwar lamarin ya sanya dole aka sauke duka fasinjoji dake cikin jirgin

Labarai Makamanta

Leave a Reply