An Samar Da Maganin Ciwon Zazzabin Lassa A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar da ke inganta tsirrai da dabbobi ta Najeriya ta ce ta yi nasarar samar da maganin zazzabi Lassa, wanda ke halaka al`umma a wasu kasashen Afirka, ciki har da Najeriya.

Zazzabin Lassa dai ba shi da wani magani sadidan, cuta ce wacce ta daɗe tana kisa a Najeriya wadda aka tabbatar da ɓeraye ne ke haddasa ta.

Amma yanzu hukumar ta ce jami`anta sun gano maganin, bayan shafe shekara shida suna gudanar da bincike, kuma a halin da ake ciki yana matakin gwaji.

Labarai Makamanta

Leave a Reply