An Sako Ɗaliban Jami’a 9 Bayan Biyan Kuɗin Fansa

An sako daliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya su tara da aka yi garkuwa dasu a makon da ya gabata. An yi garkuwa da su ne a wani hari da aka kai wa masu motoci a babbar hanyar Kaduna-Abuja.

Daya daga cikin daliban mai suna Dickson Oko ya tsere amma ya samu rauni sakamakon harbin bindiga, ya ce dama masu garkuwan sun tuntubi iyalan daliban sannan suka bukaci naira miliyan 30 kafin a saki kowannensu.

Amma daga baya masu garkuwa da mutanen sun rage kudin fansar zuwa naira miliyan daya kan kowani dalibi. Da yake zantawa da jaridar TheCable a ranar Lahadi, Ashiru Zango, Shugaban tsaro na ABU, ya ce sun samu bayanin cewa an sake su amma dai har yanzu suna jiran cikakken bayani daga Shugaban bangaren harshen Faransa. Rahoton ya nuna cewa Zango ya bukaci a kara tuntubarsa a nan gaba. “Har yanzu ina jiran cikakken bayani daga Shugaban bangaren (Faransa).

“Amma wani ya fada mani cewa an sake su,” in ji shi. Bugu da kari, wani mai suna Julius Mutum wandda ya bayyana cewa shi dan uwan daya daga cikin wadanda aka sace, ya wallafa a shafin Twitter cewa an saki yar’uwarsa. “Wasu daga cikin yan ABU 9 ciki harda kanwarta sun samu yancinsu. Yan uwa ne suka yi fafutukar. Muna godiya @TheAbusite a kan daga muryoyinku da kuka yi a lokacin da gwamnati da jami’an tsaro suka ki yin komai,” ya wallafa.

A baya mun ji cewa wasu garkuwa da mutane sun sa kudin fansa a kan ‘daliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da aka sace a kan hanyar zuwa garin Abuja. Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa miyagu sun nemi a biya Naira miliyan 270 kafin su fito da wadannan ‘dalibai har tara da su ka tsare.

Labarai Makamanta

Leave a Reply