Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa, aby sake za?en shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS karo na biyu cikin shekara guda.
Sauran shugabannin ECOWAS, sun yanke shawarar sake za?arsa a taron ?ungiyar karo na 65 wanda ya gudana a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Lahadi.
Tinubu, cikin jawabinsa bayan sake za?arsa a matsayin shugaban ECOWAS, ya ce zai ci gaba da jan ragamar ?ungiyar domin kawo sauye-sauye masu alfanu.
“Na amince na ci gaba da jan ragamar shugabancin wa?annan maza da mata masu nagarta a wannan tafiya, domin inganta dimokura?iyyarmu da muka gada.”
A lokacin wa’adin Bola Ahmed Tinubu na farko, a matsayin Shugaban ECOWAS, an fuskanci juyin mulki a wasu ?asashen mambobin ?ungiyar.
Hakan ya sanya ECOWAS ?o?arin ci gaba da dawo da Nijar, Mali, da Burkina Faso cikin ?ungiyar, bayan a baya sun bayyana ficewarsu daga cikinta.
Duk da ?o?arin ECOWAS, ?asashen sun sake jaddada ?udurinsu na ficewa daga cikinta.
Idan ba a manta ba, ?asashe irin su Nijar, Burkina Faso da Mali sun fuskanci juyin mulki daga sojoji, wa?anda suka ham?arar da gwamnatin fararen hula a ?asashen.
Hakan ne ya sanya ECOWAS yin barazanar ?aukar matakin soji musammam a Nijar matu?ar sojoji ba dawo da mulkin demokura?iyya a ?asar ba.