An Sake Bude Layukan Sadarwa A Zamfara

Rahotanni daga Gusau babban birnin Zamfara na bayyana cewarGamnatin jihar ?arkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ta sanar da bude layukan sadarwa a Gusau babban birnin Jihar.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Ibrahim Dosara ne ya tabbatar wa da BBC hakan.

Dosara ya ce baya ga bude layukan wasa an kuma bude kasuwar gusau wadda ita ma a baya aka sanar da rufe ta.

“An sauya dokar takaita zirga-zirga ababan hawa daga 8 na yamma zuwa 6 na safe a baya, zuwa 6 na safe zuwa 12 na dare”.

A iya cewa dai wannan wata manunuiya ce ta nasarar da gwamnatin jihar take samu a yakin da take yi da ‘yan bindiga a Zamfara.

Kamarin da matsalar tsaro ta yi a Zamfara ne ya sanya hukumomin jihar toshe layukan sadarwa na tsawon wata guda, domin shawo kan lamarin.

Sai dai Dosara ya ce iya tsakiyar birnin Gusau ne kawai wannan lamari ya shafa.

Related posts

Leave a Comment