An Rantsar Da Samia Hassan A Matsayin Shugabar Kasar Tanzaniya

An rantsar da Samia Suluhu Hassan a matsayin mace ta farko Shugaabar ?asar Tanzania biyo bayan mutuwar John Magufuli ranar Laraba.

Al?alin Al?alai Ibrahim Juma ne ya rantsar da ita a Fadar Gwamnati da ke babban birnin ?asar Dar es Salaam.

Ita ce shugabar Tanzania ta shida bayan ta shafe shekara fiye da biyar a matsayin mataimakiyar Magufuli, wanda ya rasu sakamakon ciwon zuciya.

Kundin tsarin mulkin Tanzania ya tanadi cewa mai shekara 61 ?in za ta ?arasa wa’adi na biyu na shekara biyar da suka fara.

Ita ce shugabar ?asa mace tilo a Nahiyar Afirka da ke kan mulki yanzu haka.

A bangarorin duniya da dama Mata na cigaba da nuna murna da farin ciki da shigabancin da Malama Samia Saluhu ta samu,inda suke kallon nasarar ta ta a matsayin nasara ga dukkanin Mata.

Related posts

Leave a Comment