Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta kori wata mata mai mukamin kofur (corporal) mai suna Olajide Omolola bayan ta yi ciki kuma bata da aure.
A wani rahoto da jaridar Punch ta fitar, hukumar ‘yan sandan ta sanar korar jami’ar a wani sako da ya fito daga sashen kudi da tsare tsare na hukumar a Ado Ekiti.
An tura takardar ga DPO na Iye Ekiti inda Omolola ta ke da zama. A cikin sakon, an umarci mai kula da harkokin kudi a Ekiti da ya tabbatar ya bada bayanan ga IPPIS don tabbatar da an dakatar da albashin ta.
“Sashe na 127 na dokar aikin ‘yan sanda da ya hana mata ‘yan sanda daukar ciki kafin aure na kunshe cikin takardar sallamar kofur Olajide Omolola wacce ta kammala makarantar horon yan sanda ranar 24/04/2020, ” kamar yadda takardar ta nuna.
“An sallame ta daga aiki sannan a karbe duk wasu takardu nata da suka shafi aikin ‘yan sanda nan take kamar yadda hukumar ta bayyana.
“Omolola ta kammala makarantar horar da yan sanda 24 ga watan Afrilu, 2020, kuma an tura ta Iye Ekiti.
Sashe na 127 na aikin ‘yan sanda na cewa, “duk jami’ar yan sanda mace da tayi cikin kafin auren ta a sallame ta daga aiki, kuma kar a sake daukar ta sai da sahalewar babban sufeto na kasa.”