Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an sake duba shirin ciyar da yaran makaranta a Najeriya inda aka duba shi tare da kara N30 kan N70 na kudin abincin ‘yan makaranta a jihar Delta da wasu Jihohi.
Kwamishinan jin kai da tallafi na jihar Delta Dakta Darlington Ijeh, wanda ya bayyana hakan a Asaba, ya bayyana takaicinsa kan yadda masu dafa abincin ke kauro.
Dakta Ijeh, wanda Gwamna Ifeanyi Okowa ya rantsar a watan Augustan 2022, ya sha alwashin lura da shirin gwamnatin tarayyan domin inganta rayuwar jama’ar jihar.
Kwamishina ya bayyana kalubalen da ya fuskanta game da ciyarwar ‘yan makaranta Yace: “Bayan shigata ofis a watanni uku da suka gabata, na gaji wasu lamurran koma baya daga NHGSFP da ya hada da rashin biya kan lokaci, da sauran matsalolin da suka shafi masu girkin wadanda ke taba dalibai dake jihar.
“A yau an sake duba N70 na abincin kowanne ‘dan makaranta inda aka mayar N100 kowanne da kuma sauran matsalolin da suka addabi tsarin ciyar da ‘yan makaranta a jihar kamar rashin masu girkin da biya ba bisa tsari ba, sun zama tarihi.”
Kwamishinan wanda ya raba kayan abinci ga masu girkin yayi kira garesu da su mayar da halayya tagari ta zama jagoran aikinsu, yace tsarin ciyarwan an yi shi ne domin ciyar da ‘yan makarantun gwamnati daga aji 1 zuwa 3 inda ya kara da cewa an yi hakan ne domin karfafa guiwar iyaye wurin sanya yara a makaranta tare da inganta abincin dalibai.