An Gano Tulin Muggan Makamai A Jos Babban Birnin Jihar Filato

IMG 20240308 WA0095

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun gano makamai masu yawa na zamani da kuma ƙirar gida a gundumar Fann da ke yankin ƙaramar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato.

Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar sun ce sun ƙaddamar da samame a ƙauyukan gundumar ne bayan da wasu ɓata-gari suka kashe wani jami’in shige da fice a lokacin da jami’an tsaro ƙarƙashin rundunar Operation SAFE HAVEN ke sintiri a yankin.

An ce ɓata-garin sun kashe jami’in a lokacin da yake duba motarsu wadda aka yi zargin sun ɗauko makamai a cikinta.

Bayan haka ne jami’an sojojin suka ƙaddamar da samame da nufin gano makamai tare da kama mutanen da ake zargi da hannu a lamarin.

”Bayan shafe mako guda, dakarunmu sun kama mutum takwas tare da gano makamai na zamani da kirar gida a ƙauyukan Ratas da Ratoso da kuma Sangasa duka a gundumar Fann da ke yankin ƙaramar hukumar Barikin Ladi”, in ji sanarwar.

Makaman da aka gano a lokacin samamen sun haɗa da:

Bindiga ƙirar AK-47, 12 da samufurin AK-47 ƙirar gida 12, da ƙanannan bindigogi 15 da kwanson harsasan AK-47 15 da kakin soja, da harsasai 250 da sauran makamai da kwari da baka da babura bakwai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply